Marigayi San Nda-Isaiah mawallafin jaridun Leadership

Marigayi San Nda-Isaiah mawallafin jaridun Leadership

Mawallafin jaridun Leadership da ake bugawa a Najeriya Mista Sam Nda-Isaiah ya mutu.

Iyalan marigayin sun sanar da BBC cewa ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren jiya Juma’a bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Mista Sam ya mutu yana da shekara 58.

A wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya Femi Adeshina ya fitar, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Nda-Isaiah a matsayin aboki kuma na hannun damansa na siyasa.

Shugaba Buhari ya kuma mika sakon gwamnatin Najeriya ga daukacin ‘yan jaridu Najeriya da iyalan gidan marigayin da kuma makusantansa kan wannan babban rashin.

Abin da ya sa Dattawan Arewa suke so Buhari ya sauka daga mulki
Mutuwar Isma’ila Isa Funtua ta bar babban giɓi – Shugaba Buhari
Marigayin ya taba tsayawa takarar shugabancin Najeriya tare da shugaba Buhari a zaben shekarar 2015. Kafin rasuwarsa, shi ne ke rike da sarautar Kakaki Nupe.

An haifi Mista Sam Nda-Isaiah ne a Minna, babban birnin jihar Neja a 1962, kuma ya halarci jami’ar Obafemi Awolowo inda ya karanci ilimim hada magunguna.

Marigayi Nda-Isaiah fitaccen dan jarida ne kuma inda ya dade ana wallafa ra’ayoyinsa a jaridar Daily Trust kafin daga baya ya kafa jaridarsa mai suna Leadership a shekarar 2001 wadda ke wallafa labarai cikin harsunan Ingilishi da Hausa.

Comments are closed.